Kasafin 2017 Zai Fitar Da Nijeriya Daga Yanayin Kunci – BuhariShugaba Muhammad Buhari ya nuna cewa yana da tabbaci kan cewa kasafin kudi na shekarar 2017 zai fitar da Nijeriya daga yanayin kunci tare da farfado da tattalin arziki da ya rigaya ya karye.
Buhari ya yi wannan ikirarin ne a sakonsa na bikin Maulud, inda ya kalubalanci ‘yan Nijeriya kan kada su yanke tsammani bisa kokarin da gwamnatinsa ke yi na ganin ta inganta rayuwar al’ummar kasar nan.

Ya kara da cewa ya kamata ‘yan Nijeriya su yi amfani da wannan yanayi a matsayi wani kalubale na hadin kan kasa tare da yin aiki tukura wajen tallafawa kokarin da gwamnati ke yi.

You may also like