Kasafin Ayyukan 2017 Da Gwamna Ganduje Na Jihar Kano Ya Gabatar. Gwamnan jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje ya gabatar da daftarin kasafin kudin 2017 na Naira Bilyan N209, da milyan 857, da dubu 330, da dari 488 a gaban majalisar dokokin jihar domin tabbatarwa.
Kasafin na badi mai taken “Dogaro da kai mai dorewa” ya kunshi Bilyan N130, da milyan 486, da dubu 682, da dari 677 na manyan ayyuka sai kuma Bilyan N79, da milyan 370, da dubu 647, da dari 811 na ayyukan cikin gida.
 

A cikin wata sanarwa da kakakin fadar Gwamnatin jihar Kano, Alhaji Salihu Tanko Yakasai ya fitar yace fannin ayyuka da gidaje keda kaso mafi rinjaye na Bilyan N43.72, wanda ya kunshi gina hanyoyi da gadoji a birane da kauyakun jihar, da gina Kwata ta yankan dabbobi ta zamani a birnin Kano da kuma kammala wasu gadojin kasa da kuma soma gina tashoshin jirgin kasa da dai sauran ayyuka daban-daban. 
 

Sanarwar tace fannin ilimi ne ke biye da Bilyan N17. 5, sai fannin Kasa da Sufiyo keda Bilyan N16. 8, sai fannin albarkatun ruwa keda Bilyan N13. 5 a yayinda kiwon lafiya aka ware masa Bilyan N10. 74.
 

Gwamnan ya kuma ce fannin noma da aikace-aikace an ware masa Bilyan N6.6. A yayinda fannin kula da muhalli keda Bilyan N1.7, sai fannin kudi da kere-kere keda Bilyan N1.7 sai fannin watsa labarai da wasanni wanda aka ware masa Bilyan N1.25.
 

Sauran fannonin sun hada da ma’aikatar harkokin mata da cigaban Al’umma wanda aka warewa Milyan N854 sai kuma fannin mulki da ayyukan majalisa da aka warewa Milyan N702.

 

Da yake karbar daftarin kasafin jim kadan bayan Gwamnan ya kammala gabatarwa, Kakakin majalisar Dokokin jihar, Alhaji Kabiru Alhasan Rurum ya sha alwashin jin ra’ayoyin jama’ar jihar akan kasafin tare. Yana mai cewa kasafin zai samu kyakkyawan kulawa a majalisar.

You may also like