Gidan mataimakin shugaban kasa dake fadar shugaban kasa ya ware naira miliyan ₦17 domin sayan tukwanen dafa abinci, cokula farantai da sauransu a kasafin kudin shekarar 2018.
Bayan wannan kuɗin za a kashe naira miliyan ₦50 wajen sayan kayan abinci da sauran kayan girki da kuma karin miliyan ₦18 ta lemuna da sauran abin sha.
Naira miliyan ₦2.3 za kashe wajen siyan makamashin gas na girki.
Gidan shugaban kasa ya ware naira 145 wajen sayan kayan abinci da sauran kayayyakin girki da kuma naira miliyan ₦135 wajen sayan abin sha.
Naira miliyan ₦18 aka ware wajen sayan makamashin girkin gas.