Shugaba Muhammad Buhari ya umarci shugabannin hukumomin gwamnati kan su gaggauta bayyana gaban majalisar tarayya don yin bayani game da bukatun da suka gabatar a cikin kasafin kudin bana.
Shugaban ya bayar da wannan umarnin ne a jiya bayan da shugabannin majalisar a karkashin jagorancin Sanata Bukola Saraki suka ziyarce shi a fadarsa inda suka koka kan yadda shugabannin hukumomin gwamnati ke kin bayar da hadin kai ga majalisar a kokarin da take yi na ganin ta kammala aikin kasafin kudin.