Kasan Jikinka: Baiwar da Allah ya yiwa hannunkaA kowacce rana Allah ne kadai ya san sau nawa ka ke ko ki ke amfani da wata gaba ta musamman a jikinku, ba dare ba safiya ballantana dogon tunani na yadda za ka yi ko za ki yi ki yi amfani da ita.

Kullum za ka yi alwala da wannan gabar, ka ci abinci, ka sauya kaya, ka ta je kai, ki yi kitso, ki dafa abinci da sauransu. To, wannan gaba dai ita ce hannu.

Hannunmu gaba ce ta musamman da Rabbul izzati ya halitta ma na, domin saukake ma na al’amuran rayuwa. Yau idan Sarkin Ya so, zan fi bada himma wajen bayani a kan halittar da Allah ya yiwa hannu.

Hannunka ya na da abubuwa da yawa, wadanda da Hausa ni kaina ban san sunansu ba, sai dai na yi iya kokarina wajen wassafa ma na su ta yadda za mu iya hasaso su a ranmu.

Daya daga cikin darajar da hannu ke da ita shi ne, da shi Allah ya sa dan Adam ya fi sauran halittu ko kuma ya zama jagoransu, saboda ya na sarrafa hannunsa ta hanyoyi masu ban mamaki.

Da farko dai fatar tafin hannunka ko hannunki ta musamman ce mai kauri. Bayan nan, a na samun irinta a tafin kafa. Sannan zanen da ke cikin tafin hannunka, kai kadai ne mai irinsa duk duniya. Idan ku ka duba da kyau, za ku ga tafin hannu ya dan loba ko na ce ya yi kwari kadan wanda hakan na da sirri. Kadan daga ciki shi ne ba mu damar kamawa da rike abubuwa.

Idan ku ka kalli yatsunku da kyau, ba kansu daya ba, wani ya fi wani tsayi. Wannan wata gwaninta ce ta Ubangijin halitta. Da Ya so da sai Ya yi su kai daya. Idan da yatsun hannayenmu kai daya su ke, to damka da fizga da rike abubuwa ba zai yiwu a gare mu ba.

Daga wuyan hannu zuwa yatsu, akwai mahadar kashi wanda yawansu ya fi 20. Kasusuwan da su ke zaune a wuyan hannu guda takwas ne; a na kiran su ‘carpal bones’ da Turanci. A samansu kuma kashin yatsun hannu ne kai tsaye ke makwabtaka da su.

Kowanne yatsan hannu ya na da kashi guda hudu, amma babban yatsa ya na da guda uku ne kawai. Kenan kowanne yatsa ya na da mahada guda uku, shi kuma babban yatsa ya na da guda biyu; jumulla, mu na da mahadar kashi guda 14 kenan da kuma kashi takwas na wuyan hannu; ga 19 na tsintsiyar hannu, kun ga 28 kenan.

Hannu ya na da tsoka dai-dai har guda goma 18, Kuma kusan kowacce da aikinta, duk da cewa a cikinsu, wasu guda biyu ko kuma guda uku, su na aiki iri daya ne. Nan gaba kadan za mu ga irin aikin da su ke yi.

Bututun jinin da da ya kawo wa hannunka jini guda biyu ne, amma tushensu guda daya ne, wani bututun jini ne da ke a tsakiyar damtse da a ke kira “Brachial artery”.

A daidai gwiwar hannu, sai wannan hanyar jini ta rabe gida biyu, wato ‘radial artery’ a bangaren babban yatsa da ‘ulnar artery’ a bangaren dan karamin yatsa. Wato daya a bangaren dama, dayar kuma a dangaren hagu. Da shigarsu cikin tafin hannu, sai su ka yi wata kawanya, su ka hade da juna sannan su ka sake fidda rassa.

Ka yi tunanin me ya sa likita ko malamin jinya (nurse) kan tada wuyan hannu, kusa da tushen babban yatsa idan mutum ya mutu? Amsar ita ce domin su tabbatar ya mutu. Akwai bututun jini a wajen wanda a ke kira “radial artery”. Wato na bangaren babban yatsa wanda idan zuciya ta harbo jini, wucewar jinin ta cikinsa ya na sa wa ya motsa ko ya harba. Wannan shi a ke kira “pulse”.

Wata kayatacciyar gwanintar ita ce, an yi wa yatsunmu ado da farata (farce), domin su kawata yatsun hannayenmu. Ka yi tunani ya munin hannun mu zai kasance idan kawai haka yatsunmu su ke, babu farce?

Farce ya na kara kyawun hannu. Ko shin wannan ne kadai aikinsa? Amsar ku ita ce, a’a. Farce ya na kare kan dan yatsa daga cutuwa ko lahani, sannan kuma ya na bada kariya ga kwayoyin halitta masu taushi na kan yatsa. Sannan kuma ya na taimaka wa wajen gudanar da kananan motsi kamar susa, mintsini da sauransu.

Ina so na yi kokari na fada mu ku kadan daga cikin abin da na sani game da jikinmu, amma a lokaci daya kuma, Ina son idan kun karanta, ku zurfafa tunani da duba da idanun basira. Hakan shi zai kara ma na ganin girman Wanda ya yi halittar.

Idan har ka na da ko ki na da yatsu biyar, godewa Khaliki, saboda a lokacin da mu ke cikin iyayenmu, gabadaya hannayenmu da kafafuwanmu dungulmi ne; ma’ana babu alamar yatsa. To, da ya ke halittar jiki ta na bin matakai masu tsayi kuma daki-daki, akwai lokacin da Mahalicci ya ke bada umarnin a tsaga ma na yatsu.

Awonsu, tsayi da fadi da kauri da karfinsu da kuma guda nawa za a tsaga, duk Sarkin halitta ne ke tsarawa. Idan da ya so sai ya tsaga ma ka uku ko biyu, ko ya barka dungulmi, babu yadda za ka yi.

Yatsu biyar, tsoka 18, mahadar kashi 14, kasusuwa 27 lullube da fata da kitse mai tallafawa, ka san ba a banza a ka yi ma ka su ba.

A rubutu mai zuwa, za mu ga irin abubuwan da mu ke da ikon yi da wannan gaba mai tarin baiwa da izinin Sarki, wanda ya iya tsara halitta.

         Daga Mustapha Ibrahim Abdullahi


Like it? Share with your friends!

0

You may also like