Kasan Jikinka:Baiwar Da Allah Ya Yiwa Hannunka (II)



“Shin kuna tsammanin Mun halicce ku ne Dan waasa, kuma ba Gurin Mu zaku komo ba?” Kur’ani (Surah Anbiyaa’, Aya: 115.)

Yatsu biyar, tsoka goma sha takwas, mahadar kashi goma sha hudu, kasusuwa ashirin da bakwai lullube da fata da kitse mai tallafawa, kaasan ba a banza aka yi maka su ba.

A rubutun yau da Yardar Mai duka, zamu ga irin abubuwan da muke da ikon yi da wannan gaba mai tarin baiwa wato hannu.

Amma kafin nan, bara mu dan kalli ta inda hannu da yatsu suke samun tallafin motsawa. Kowanne yatsa na hannu, yana da wata doguwar halitta, mai kama da igiya, wato “Kashe Kara” da take damfare dashi. Asalin wannan Kashe kara, tsoka ce ko kuma Ince tsokoki ne wadanda suke Asalin su ya taso daga gwiwar hannu, har ya zuwa wuyan hannu.

Kafin wannan ayari na tsoka ya shiga cikin hannu, a dai-dai gurbin wuyan hannu, sai kowacce tsoka ta tsuke, ta rikide, ta zama kamar wata igiya, sannan ta zarce ya zuwa yatsan da Allah ya nufa nan ne tikewar ta.

Yayin da ka mikar da yatsun ka, ko ka tankwara su, ko kika dunkule su, wadannan tsokoki su ne ke dawainiya a ko da yaushe. Kar kuma ku manta; ga jijiyar motsi kuma da take jikin su, tana da Aikin isar da sakon lantarki daga kwakwalwa zuwa tsokar, sannan daga tsokar zuwa kwakwalwa. Sai hakan ta faru, sannan hannu zai motsa.

Yanzu zan faara ta kanka. Na san dai da hannunka kake amfani wajen budo shafin “Ka San Jikinka” Na wannan jarida; Ka taba tunanin wace tsoka da wace tsoka ke motsawa yayin da Ka dauki jaridar, ko Ka bude shafukanta? A iya tunani na, da hasashe na, kana amfani rukunin tsoka guda biyu.

Rukuni na farko, shi ne wanda ya kunshi kungiyar tsoka masu lankwasa kasangalalen hannu ciki (kamar in zaka taba fuskar ka, ko zaka taada kwanji) kimanin guda shida(6). Akwai kishiyoyin su masu mikar da hannu.

To, sai kuma rukuni na biyu: tsokokin da suke tafin hannun ka ko hannun ki. A cikin tsoka guda goma sha takwas, kuna amfani da kamar guda goma sha biyar daga cikin su. Idan kuma a waya kake/ki ke karantawa, nasan kunayin amfani da babban yatsa wajen ture abin da aka gama karantawa zuwa sama, wato “scrolling”.

A “scrolling” kawai, kuna amfani da tsoka guda hudu. Akwai mai dora babban yatsa kan gilashin wayar, Akwai mai Jan sa Idan ka gama scrolling din, Akwai mai tankwara yatsan, sannan Akwai mai mai taimaka masa (shi yatsan) wajen taba sauran yatsu; wannan wata kebantacciyar baiwa ce ta babban dan yatsa, wato iya taba sauran yatsun hannu da kansa. A takaice dai, bazan iya fada muku hakikanin wacce tsoka da wacce tsoka ce suka motsa ba, sanin hakan na ga Ubangijin halitta.

Wannan gaba tana da matukar ban mamaki da baiwa. Da ita ake sarrafa abubuwa da dama. Wasu ma, sun fi karfin a lissafo su a nan. Amma bara muga kadan daga ciki, musamman masu muhimmanci cikin su.

A na rubutu da hannu. Amma kash! Akwai rubutu mai amfani da kuma akasin haka. Lokacin da nake rubuta wannan insha’i, nasan dai nayi amfani da hannu na. Amma ban san tsoka nawa ce ta motsa ba tun daga farawa har zuwa gamawa. Ban San sau nawa jini yayi kai kawo a hannu na ba, sannan ban San sau nawa kwakwalwa tayi musayar sako tsakanin ta da tsokokin hannu na ba. Amma rashin sanin hakan, baya nuna cewa hakan bata faaru ba. Ya dan uwa, kayi nazari akan wannan batu.

Hannun nan namu kyauta ce mai matukar muhimmanci daga Khaliki. Kira, saka, fawa, aski, jima, a takaice dai kusan duk wata sana’a da ka sani, babba ko karama, hannu na taka muhimmiyar rawa wajen gudanar da ita.

Likitocin tiyata suna daukar lokaci mai tsayi domin neman kwarewa wajen yin amfani da hannun su wajen yin tiyata. Saboda yadda za’a jujjuya hannun, a sarrafa fa shi na bukatar kwarewa. Wannan yana cikin motsi na musamman Wanda ke bukatar tattara hankali waje guda.

Hannu yana taka muhimmiyar rawa wajen isar da sako. Sakon zai iya kasancewa kyakkyawa ko mummuna. Wadanda Allah ya jarrabe su da rashin iya magana, suna amfani da hannayen su domin isar da Sakon abin da ke ran su.

Mai magana ma na yin amfani da hannu wajen nuna alama a lokacin da yake magana, wato “gesture” a turance. Kar ku manta, a duk motsin da hannu ke yi cikin abubuwan da na fada da ma wanda ban fada ba, akwai tsokar da take aiki, akwai jijiyar motsi (nerbe) da take kawo sako, sannan kuma akwai kashin da tsokar take a jikin sa domin su hada kai yayin motsin.

Idan da za muyi duba da tunani mai zurfi, zamu gamsu cewa ba karamar kyauta Allah ya yi mana ba. Kuma tabbas duk abin da aka hana hannun mu ya aikata, a karshe cutar da mu zai yi, ko da mun San hakan ko ba mu sani ba.

Wannan baiwa da Rabbi yayi mana, bata gushewa; kalli wadanda aka jarraba da rashin hannu. Zaku ga cewa suna amfani da kafafun su ta hanyoyi masu ban mamaki. Kadan daga cikin abin da yasa hakan shi ne: hikimar sarrafa hannu da aiki da shi tana komawa ga kafafuwan nasu ne, saboda basu da hannu.

A karshe, shawarar da zan bamu ita ce: mu dinga kokari wajen tuna wannan ni’ima a mafi yawan lokutan da muke amfani da hannayen mu. Nima kam Alhamdulillah da ya bani damar yin amfani da hannu na wajen rubuta muku wannan dan tkaitaccen bayani game da hannayen me. Shin meye addu’arka/ addu’arki bayan kin gama karanta wannan rubutu?

Idan kuna neman sauran bayani akan “Hannu”, sai ku jira littafi na wanda zai fito nan ba da jimawa ba da izinin Sarki Mai Hikima. Sai wani satin In mai Duka Ya kaimu.

Daga Mustafa Ibrahim Abdullahi


Like it? Share with your friends!

0

You may also like