Kasar Sin Watau China ta bayyana kudirinta na zuba jari a Nijeriya na Naira Biliyan 30 don farfado da bunkasa tattalin arzikin Nijeriya.
Wannan kudirin ya fito ne daga shugaban tawagar Cibiyar Kasuwanci ta Kasar Sin mai kula da sashen Afrika, Kaftin Muhammad Joji a yayin da suka kai ziyara ga Gwamnan Bauchi a ranar Laraba.
Kaftin Joji ya ce cibiyar kasuwancin ta zabi wasu jihohi wadanda ta gamsu da salon mulkin gwamnatocinsu da yadda bincike ya nuna suna kashe kudaden jihohinsu inda jihar Bauchi ke cikinsu.
Da ya ke nasa bayani a lokacin ziyarar da suka a fadar Gwamnatin jihar Bauchi, Daraktan Cibiyar kana wanda ya jagoranci tawagar, Mista Liam, ya nuna gamsuwarsa da Gwamnatin Bauchi tare da fatan ganin an cimma yarjejeniya domin jihar ta amfana da kudaden da kasar Sin za ta bayar.
Shugaban Hukumar Zuba Jari ta Jihar Bauchi, Malam Aminu Musa ya yi wa tawagar karin haske kan bangarorin da jihar ta wadatu da su da masu sha’awar zuba jari za su iya amfana a kai kamar fannin, noma da kiwo, ma’adanai da wajajen yawan bude ido.
Gwamna Mohammed Abdullahi Abubakar ya gode wa cibiyar tare da ba su tabbacin cewa a ko da yaushe kofar jihar Bauchi a bude take domin maraba da masu sha’awar zuba jari.
A sanarwar da mataimakin na musamma a fanni sadarwa ga Gwamnan Bauchi, Shamsudeen Lukman ya bayar, ya ce, Gwamnan ya yi wa tawagar albishir cewa ‘yan majalisar jihar sun zartar dokar halasta kasuwanci ta PPP sannan suka sake saukaka hanyar karbar masu zuba jari a jihar musamman wajen bayar da filayen gina masana’antu.