Kasar Filipins za ta yi sulhu da ‘yan tawaye


Shugaban kasar Filipins ya ayyana shirin tsagaita da ‘yan tawayen masu ra’ayin Kwaminisanci.

Sabon shugaban kasar Filipins Rodrigo Duterte ya jaddada aniyarsa ta neman sulhu da masu tada kayar baya ‘yan ra’ayin Kwaminisanci da suka kwashe shekaru gommai suna dauki ba dadi da gwamnati. A cikin jawabinsa na farko ga zaman majalisar dokoki da ke birnin Manila shugaban ya sanar da shirin tsagaita wuta daga bangaren gwamnati. Ya yi kira ga ‘yan tawayen da su ma su ajiye makamansu.

Ya ce: “Ku bari mu kawo karshen wadannan shekaru gommai na tashe-tashen hankula da nuna kiyayya. Ba inda za su kai mu. Suna ma kara yin muni ne a kullum.”

Shi ma shugaban kungiyar ‘yan tawayen ta KP ya nuna shirin daukar matakin sulhun. Mutane fiye da dubu 40 aka kiyasta sun rasa rayukansu tun bayan barkewar rikicin da ‘yan tawayen masu ra’ayin Kwaminisancin a karshen shekarun 1960.

You may also like