Kasar Gambia za ta fara sayar da jiragen sama da kuma wasu motoci masu tsada da tsohon shugaban kasar Yahaya Jammeh ya saya a tsawon shekarun da ya shafe yana mulkin kasar.
Kasar ta fara daukar wannan mataki ne a kokarin da take na biyan bashin da ya yi mata katutu.
Jammeh, wanda ya kwaci mulki a wani juyin mulki da ya yi a shekarar 1994, ya bar kasar Gambia a farkon shekarar da ta wuce bayan da kasashen yankin Afrika ta yamma suka yi kokarin kawar da shi da karfin soja biyo bayan kin yarda da ya yi ya mika mulki duk da kayin da ya sha a zaben shugaban kasar da aka gudanar.
Ya yin da mafi yawan yan kasar ke rayuwa cikin talauci shugaban ya tara da dukiya mai tarin yawa.
A cewar ministan kudin kasar tuni aka saka motocin masu tsada da kuma wasu jirage uku a kasuwa.
Tuni asusun bada lamuni na duniya wato IMF ya gargadi kasar akan sake ciwo bashi.
Yanzu haka dai shugaban na gudun hijira a kasar Equitorial Guinea.