Gwamnatin ƙasar Habasha a ranar Laraba ta bada umarnin a sako dukkanin fursunonin siyasa da ake tsare da su kana kuma a rufe gidan yarin Maekalawi wanda yayi kaurin suna.
Gidan yarin ana amfani dashi wajen tsare manyan yan siyasa a kasar dake gabashin Afrika.
Firaministan ƙasar,Hailemerian Desalegn shine ya bada umarnin a wani bangare na abinda ya kira samar da haɗin kan kasa da kuma dimakwaradiya da zata bawa kowa dama.
Wannan yunkuri na baya bayannan na zuwa ne a lokacin da zanga-zangar kin jini gwamanati ke kara bazuwa a yankunan Oromia da Amhara dake fama da rikicin kin jinin gwamnati.
Fursunonin siyasa wadanda ke fuskantar tuhuma a gaban kotu dukkaninsu za a yi musu afuwa.