kasar India Na Duba Yiyuwar Daina Sayan Danyen Man Fetur Daga Najeriya Kamfanin man fetur na kasar India da ake kira Hindustan Petroleum yana duba yiyuwar daina sayan danyen mai daga Najeriya. 

Hakan na zuwa ne kasa da shekara uku bayan da kasar Amurika ta daina sayan mai daga Najeriya karkashin shugabancin Barack Obama,  Najeriya ta maida hankalinta kan kasashen Asiya musamman India da China. 

A shekarar 2015 -2016 India ta shigo da kaso 12 cikin dari na man da take bukata daga Najeriya a cewar kamfanin mai nakasa NNPC. 

Amma kamfanin dillancin labarai na Reuters ya rawaito cewa India zata fara sayan mai dake da karancin sindarin Sulphur daga kasar Amurika a watanni kadan masu zuwa.

Za ayi amfani da man a matatar mai ta Vizgag dake kudancin kasar wacce take tace ganga 166,000  a rana. 

A shekarar da ta gabata ne dai jakadan kasar India a Najeriya ya koka kan cewa Najeriya ce kasa daya da India take siyan manta ta hannun dillalai mai makon ciniki kai tsaye.

Har ila yau jakadan yakoka kan yadda kasashen biyu suka gaza cimma yarjejeniya cinikayya mai tsawo.kamar yadda kasar ta India ta shiga irin wannan yarjejeniya da wasu kasashe da take siyan mai a hannunsu.  

You may also like