Japan na bukin cika shekaru 71, da kasar Amurka ta kai mummunar hari a Hiroshima.


 

Kasar Japan na bukin cika shekaru 71, a yau da kasar Amurka ta kai mummunar hari da  makami mai linzami na nukiliya, birnin Hiroshima.

 

Bukin da suke yi duk shekara na zuwa ne ‘yan watanni bayan da Shugaban Amurka na yanzu Barack Obama ya kasance Shugaban Amurka na farko da ya ziyarci yankin na Hiroshima, don juyayin rayukar da aka yi hasara.

Da sanyin safiya ranar 6 ga watan Augusta na shekara ta 1945,  wani jirgin yaki na kasar Amurka, Enola Gay, ya saki mummunar Bam din daya kashe dubban rayukan jama’a.

Bukin na yau ya sami halarcin mutane kusan dubu 50 ciki har da Fira Minista Shinzo Abe da wasu wakilan kasashen duniya  akalla 80, inda akayi juyayi da al’adar yin shiru na tsawon minti daya don girmama mamatan.

You may also like