Kasar Kamaru Ta Sanar Da Wasu Sabbin Dabarun Fada Da Kungiyar Boko Haram


4bk9d47a8961e4eig1_800c450-1

 

Majiyoyin tsaron kasar Kamaru sun bayyana cewa gwamnatin kasar ta tsara wasu sabbin dabarun fada da kungiyar ta’addancin nan ta Boko Haram wacce ta addabi kasashen yankin.

Kafar watsa labaran Africa Times ta jiyo wata majiyar tsaron kasar Kamarun tana fadin cewa cibiyoyin tsaron kasar sun tsara wasu sabbin dabaru da nufin fada da kungiyar ta Boko Haram da nufin raunana ‘yan kungiyar da kuma dakile kaifin hare-haren ta’addancin da suke kai wa kasar.

Majiyar ta kara da cewa an dau wadannan matakan ne a yayin wani taro na tsaro da aka gudanar karkashin jagorancin magajin garin lardin arewacin kasar Kamarun bugu da kari kan kwamandojin dakarun soji da sauran na cibiyoyin tsaro.

Har ila yau kuma rahotannin sun ce an dau tsauraran matakan tsaro a kan iyakokin kasar musamnan kan iyakan Nijeriya don dakile hare-haren da ‘yan Boko Haram din suke kai wa kasar ta Kamaru.

A shekarar bara ta 2015 ne dai ‘yan Boko Haram din suka tsananta irin hare-haren da suke kai wa kasar Kamarun.

You may also like