Kasar Morocco Ta Haramtawa Mata Sanya Burka


 

Mahukunta a kasar Morocco sun haramta dinkawa, sayarwa da kuma shigo da burka kasar.

A ranar Litinin aka aika wa ‘yan kasuwa masu sayarda burkan da kuma masu dinkawa wasikun haramci, inda aka umarce su da su rabu da duk wadanda suke da shi a kasa cikin sa’o’i 48.

Sai dai kuma gwamnatin jahar ba ta fitar da wata sanarwa ba a hukumance game da wannan lamari, amma wani jami’in ma’aikatar harkokin cikin gida ta kasar ya tabbatar da haramcin a wata kafar yada Labarai ta intanet.

Jami’in ya bayyana cewa mahara suna amfani da tufar ta burka wajen aikata miyagun laifuka.

Dama dai yawanci mata a kasar na amfani da hijabi be ba burka ba, wanda shi rufe jiki yake gaba daya.

Wata kungiyar kare hakkin dan adam ta yi Allah wadai da wannan haramci, inda ta ce ta dauki dokar a matsayin wani yunkuri na tauye ‘yancin mata na sanya tufar da ta dace da addininsu ko siyasarsu ko al’adarsu.

You may also like