Kasar Rasha Ta Ki Amincewa Da Bukatar Kara Wa’adin Dakatar Da Bude Wuta A Kasar Siriya


 

Kasar Rasha ta ki amincewa da bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta neman kara wa’adin dakatar da bude wuta a garin Halab dake arewacin kasar Siriya.

Kakakin ma’aikatar tsaron kasar Rasha Igor Kvnashnkvf a jiya Alhamis ya bayyana cewa: Bukatar Majalisar Dinkin Duniya ta neman sake kara wa’adin dakatar da bude wuta a garin Halab da ke arewacin kasar Siriya da nufin ci gaba da aikewa da kayayyakin jin kai ga al’ummar da suke yankin gabashin garin, bukata ce da bata da amfani.

Igor ya kara da cewa: Kara wa’adin dakatar da bude wutan yana matsayin taimakawa ‘yan ta’adda ne da suke mamaye da yankin gabashin garin na Halab. Yana mai fayyace cewa: Tun bayan cimma yarjejeniyar dakatar da bude wuta a garin na Halab an shigar da kayayyakin jin kai da suka kai Tan fiye da 100 lamarin da zai kai ga wadatar da al’ummun yankin ciki har da na gabashin garin.

You may also like