Kasashe 10 Da Suka Fi Hadari A Afirka


Africa

Daga Bello Hamza.

 

Akwai kasahhe goma da suka fi hadari a Afirka, sakamakon rashin zama da kuma wadansu hadu da za aiya fuskanta a cikinsu. Mafi yawan wadannan kasashen suna cikin bala’in yaki da kuma rashin kwanciyar hankali ta fuskar siyasa da ayyukan ta’addanci da kuma take hakkin bil’adama. An zayyana sunan kasshen guda goma ne wata takardar rahoto ta shekarar 2012 na kasshe masu zaman lafiya a duniya. Rahoton ya kasa kasashen duniya zuwa kashi 153  kan yadda zaman lafiya yake a duniya. Rahoton na shekara 2012, cewa, a halin yanzu ana kara samun zaman lafiya a duniya, idan aka kwatanta da shekarun baya. An bayyana kasashe goman da suka fi hadari a duniya da cewa, kasashe da rikicin da ayyukan ta’addanci suka dabaibaye su. Wadannan kasashen kuwa su ne:

  1. Habasha Ethiopia

Kasar Habasha ita ce ta goma a cikn jerin kasshen Afirka  da suka fi hadari. Ethiopia has been Kasar na gwabza yaki tsakannta da Eritiriya fiye da sheaka goma. Eritiriya ta samu ‘yanci daga Habasha tun shekara talatatin da suka wuce, bayan sun dade suna yakin nean ‘yancin kansu. An fara yaki tsakanin Habasha da Eritiriya ne sakamakon shata kan iyakar da kasar ta Eritiriya ta yi a shekarar 1991.  Duk da cewa,Kotun duniya fitar da iyaka tsakanin wadannan kasashe, har yanzu ba su da jituwa a tsakaninsu, saboda Habasha ta ki janye wa daga yankin

Akwai kuma wara kungiya da ake kira Oromo Liberation Front wadda kungiya ce ta ‘yanta’adda da ake zargin gwamnatin Habasha ce ta kafa ta. Wani makishin kasa da ake kira Oromo ne ya kafa kungiyar ce a shekara ta1973 ta niyyar kwato hakkin ‘yankabilarsu karkashin mulkin mallakar Abbaseniyawa.

  1. Burundi

Shekara goma sha biyar da suka wuce kasar Burundi ta yi kaurin suna wajen rkice-rikcen siyasa, kuma an dade ana kokarin tattauna wa a kan wannan matsala. Kungiyoyin kasashen waje dana cikin gida sun ta kaoarin ganin an kawo karshen wadannan rikice-rikce mai makon ma a samu sauki abin kullum sai kara lalace wa yake yi wanda kuma aka fahinci cewa, masu ra’ayin siyasa ne ke kara rura wutar rikicin.

  1. Zimbaguwe

Sakamakon da ya biyo bayan zaben shugaban kasa a shekara ta 2008 tsakanin Robert Mugabe da Morgan Tsbangirai, wadan kowannensu ke ikirarin samun nasara tun a zagaye na farko kasar Zimbaguwe ta fada cikin rikin siyasa, inda aka samu shugannin guda biyu, Robert Mugabe na ikirarin zama shugaban kasa, yayin da shi Morgan Tsbangirai  ke ikirarin zama Faraminista a shekara ta 2009.

Aikin tattara bayanan zaman lafiya na Zimbabwe ya bayar da rahoton cewa, kashi 15 daga cikin dari na take hakkin bil’adama ana alakanta shi da zaben 2012 da kuma shekara biyun baya lokacin da aka yi wa yunkurin  na gyara tsarin mulki zagon kasa, inda aka dinga kama jama’a ana kulle su  aka haramta tarurruka., wanda kuma shi ne musabbabin jefa kasar cikin tashin hankali da karayar tattalin arziki.

  1. Chadi

Chadi ta samu ci gaba sakamakon kyakkyar dangantakarta da ksashen da ke makwantaka da ita. Fadan kabilanci da yaki tsakanin jami’an tsaron gwamnati da kungiyoyin adawa na daga cikin abubuwan da suka haifar da tashe-tashen hankula a wannan yanki. Akwai rahoton da ke cewa, kusan ‘yakasar Kanada180,000 aka tarwatsa su daga muhallinsu, ‘yan kasar Chadi 285,000 suka yi gudun hijira zuwa kasar Dafur da wasu kasashe a yakin Sudan cikin shekara uku domin gujewa tashin hankali, haka kuma wasu alummu 700,000 sun samu kan su cikin halin ni ‘yasu sakamakon rikice rikice da ta ki ci ta ki cinyewa a kasar.

  1. Nijeriya

Nijeriya kasa ce da ke da al’umma kusan miliyan 155, tana fuskantar rikice-rikice da suka shafi siyasa da zamantake wa da na tattalin arziki. A Arewaci da tsakiya kasar ta fi fuskantar rikice-rikice, musamman a ‘yan shekarun nan sakamakon karuwar rikicin da ya shafi addini, Musulinci da Kiristanci, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 20,000, haka kuma akwai karuwar aikin ‘yanta’adda da take hakkin bil’adama. Ga kuma yukurin ‘yan Neja-Delta a kudancin kasar. Ga kuma ayyukan garkuwa da jama’a da kuma hare-hare kan bututun mai. Kokarin da gwamnati ke yi na tabbatar da ‘yancin dan adam ya taimaka wajen rage wadannnan tashe-tashen hankula,da  yaki da cin-hanci da rashawa da kuma yaki da masu garkuwa da jama’a.

  1. Libiya

Rikicin kasar Libiya ya ja hankalin al’ummar kasashen waje don neman bayani kan yadda ake gallazawa ‘yankasar, wanda kuma ya haifar da zanga-zangar da ta yi sanadiyyar kifar da gwamnatin Muammar Gaddafi a gabashin kasar. Tun daga wannan lokacin ne  kasashen waje karkashin jagorancin kungiyar NATO suka tsoma baki, wanda kuma har yanzu hakarsu ta kasa cim ma ruwa.

  1. Jamhuriyar Afirkan ta tsakiya.

Duk da yarjejeniyar zaman lafiyar da aka kulla a 2008, wadansu kungiyoyin ba su yarda da wannan yarjejeniya ba, saboda haka, sun ci gaba da ba-ta-kashi a tsakaninsu. Baya nan tsaro daga Afirka ta tsakiya, sun tabbatar da cewa, rikicin ya ci gaba da balle wa yayin da kungiyar ‘yanta’adda suka kara shiga cikin babban birnin kasar watau, Bangui. A kudu maso gabashin kasar, kungiyar da wani soja Joseph Kony, ke jagoranta ta ci gaba da fafata wa. Wannan kungiyar na daga cikin manyan kungiyoyin da suka yi kaurin suna na tashin hankali a duniya, kuma kasancewar ta a  ya kara dagula al’amuran zaman lafiya a yankin.

3 Jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango.

Jerin bincike da nazarin  cibiyar bincike ta IRC daga cikn babban bala’in da duniya ta fuskanata shi ne kiyasin da aka yin a kashe mutum sama da milyan biyar  a sakamakon rikice-rikice a kasar Kwango tun shekarar 1998. Dubban ‘yangudun hijira daga Ruwanda sun kwarara zuwa kasar Kwango ta kan iyakarta, wanda ya haifar da rikice-rikce. Akwai kungiyoyin da keda a laka da al-Ka’ida da suka samu dammar shiga kasar ta wannan hanya, wanda kuma ya taimaka wajen tayar da kayar baya a kasar.

  1. Sudan

Kasar Sudan ta yi fama da rikice-rikicen cikin gida, da kuma take hakkin bil’adama tsawon lokaci wannan matsalar ta ci gaba da faru wa inda abin ya kazance cikin shekara biyu da suka wuce. Rikici ya ci gaba da ruruwa ta kan iyakar kudancin Sudan. Haka kuma cututtuka a Darfur  ya  yi sanadiyyar mutuwar mutum 300,000. mutum sama da miliyan biyu sun rasa gidajensu

  1. Somaliya

Sama da shekara 20, Somaliya ke ciki yakin basasa. Akwai rikici tsakanin gwamnatin kasar wadda da ke da goyon bayan kasar Turai da kuma ‘yan’adawa wadanda yawancinsu ‘yan’alka’ida ne.

Gwamnatin Shaikh Sharif Sheikh Ahmed ita da iko a wani bangaren babban birnin kasar watau, Mogadishu, wanda kuma ya haifar da yaki da sauran kungiyoyin kasar. Sakamakon haka, aka samu dubban ‘yangudun hijira daga wannan kasa. Kuma tana cikin kasashen yammacin sahara da ke fuskantar yaki shearu goma da suka wuce.

You may also like