Kasashe 150 sun cimma matsaya kan tunkarar matsalar dumamar yanayi


 

 

 

Wakilan kasashe sama da 150 ne suka hallara a kasar Rwanda inda suka rattaba hannu kan yarjejeniyar da ta shafi yadda za a tunkari matsalar dumamar yanayi a duniya

Wannan zai bayar da damar yi wa yarjejeniyar birnin Montreal da aka kulla a baya kwaskwarima ganin dukkanin kasashen musanman masu hannu da shuni sun amince su rage yawan turirin da ke gurbata yanayi a duniya.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da ya taimaka wajen cimma yarjejeniyar ya ce wannan abin alfahari ne ga dukkan Duniya.

Bincike dai ya nuna cewa yawan hayakin da ake fitarwa a sanadiyar ababen hawa da girki da wasu hanyoyi na anfani da wasu na’urar abinci na taka mahinmiyar rawa a gurbata yanayi.

You may also like