Kasashe mambobin OPEC sun amince da rage yawan man da suke fitarwa kowacce rana


 

 

 

Kasashe mambobin OPEC sun amince da rage yawan man da suke fitarwa kowacce rana inda a yanzu suka bayyana cewa, za su dinga fitar da ganga miliyan 32.5 kowacce rana.

A baya dai kasashen na fitar da ganga miliyan 33.24.

An dauki matakin ne sakamakon halin da kasashen Najeriya, Iran da Libiya ke ciki.

Shugaban Kungiyar ta OPEC Muhammad Bin Salih Al-Sade ya ce, za a gudanar a wani taro a watan Nuwamba don yanke hukuncin karshe.

Akwai kasashe 14 da ke cikin kungiyar OPEC wadda aka kafa a ranar 14 ga watan Satomban shekarar 1960.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like