Kasashen Amurka,Faransa da Burtaniya na ci gaba da goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda a Siriya


 

Rasha ta yi alawadai kan goyon bayan da kasashen Amurka, Faransa da Burtaniya ke baiwa Kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya

 

Kamfanin dillancin labaran Irna na kasar Iran ya nakalto Maria Zakharova kakakin Ma’aikatar harakokin wajen Rasha na cewa ci gaba da goyon bayan da kasashen Amurka, Faransa da Burtaniya ke baiwa kungiyoyin ‘yan ta’adda a kasar Siriya shi ne ya hana a sanya kungiyoyin Ahrarur-Sham da Jaishul-islam sahun kungiyoyin ‘yan ta’adda na Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya.

Kakakin Ma’aikatar harakokin wajen Rashan ta kara da cewa Masco ta rubutawa Kwamitin haramta kungiyoyi na Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya cewa ya kamata a haramta duk wata kungiya da take da alaka da kungiyoyin ta’addanici na ISIS da Alka’ida kuma a kwai kwararen shaidu dake nuna cewa kungiyoyin Ahraru Sham da Jaishul-islam su nada alaka da wadannan kungiyoyi.

Har ila yau Madam Zakharova ta ce kasar Rasha ta nada shaidu da dalilai dake nuna cewa kungiyoyin Ahraraur sham da Jaishul-islam sun cancanci a sanya su a jerin kungoyoyin ‘yan ta’adda na Duniya domin Rasha ta gabatar da kwararen dalilai dake tabbatar da cewa wadannan kungiyoyin su nada alakar kut da kut da kungiyar ta’addancin nan ta Jabhatu-Nusra dake cikin kasar ta Siriya.

You may also like