Kasashen duniya sun la’anci harin Istanbul


4bmt1125e772f6keea_800c450

 

Kasashen duniya sun la’anci harin da aka kai a Ortaköy na Istanbul wanda yayi sanadiyyar mutuwar mutane 39 tare da aika gaisuwar ta’aziyya.

Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya mika gaisuwar ta’aziyya ga Turkiyya inda ya ce, abin bakin ciki ne a kashe mutanen da basu da wani laifi.

Obama ya kuma bayyana cewa a shirye yake wurin bada kowanne taimakon da Turkiyya ke nema.

Kakakin jami’an tsaron fadar White House Ned Price kuma ya fitar da wata sanarwa inda ya ce, “Amurka na la’anatar mummunar harin da aka kai a garin Istanbul.” Inda ya kuma ce, zasu ba Turkiyya hadin kai wurin yaki da ta’addanci a matsayinsu na mamba a NATO.

Ministan harkokin waje Canada Stephane Dion kuma ya ce,

“Canada na mika gaisuwar ta’aziyarta ga iyalen wadanda suka rasa rayukansu a mummunar harin da aka kai a Istanbul kuma fatarmu wadanda suka samu raunuka kuma su warke.”

Shugaban kwamitin musulman Amurka (CAIR) Nihad Awad kuma ya fitar da sakon,

“Zuciya ta na tare da iyalen wadanda aka kashe da kuma wandanda jikkata a cikin harin da aka kai a Istanbul.”

Sakatare Janar na Rundunar tsaro ta NATO Jens Stoltenberg kuma ya fitar da wata sanarwa a ya shafin sada zumuta inda ya ce, “An fara shekarar 2017 da labarin bakin ciki. zuciyata na tare da mutanen da suka rasa rayukansu a cikin mummunar harin da aka kai a Istanbul.”

Bayan haka kuma wakiliyar Tarayyar Turai  Federica Mogherini kuma ta fitar da na ta sanarwar game da harin da aka kai a Istanbul inda ta ce,

“Zuciyata na tare da wadanda suka rasa rayukansu. Zamu ci gaba ga yi ayyuka domin hana irin wannan al’amurra faruwa.”

Bayan haka kuma shugabanin duniya da dama sun aike da gaisuwar ta’aziyyarsu a Istanbul.

You may also like