KASASHEN MUSULMI SUN HADA KAI DON LADAFTAR DA AMURKA DA ISRA’ILA KAN BIRNIN QUDUS



A halin yanzu kasashen Musulmi na taron koli a Babban birnin Turkiyya wato, Istanbul don lalubo matakin da za su dauka kan Amurka da Isra’ila bayan da Shugaban Amurka, Donald Trump ya fito fili ya amince da birnin Jeresalem a matsayin Babban birnin Isra’ila.

Haka ma, Sarkin Saudiyya, Salma Ibn AbdulAziz ya bayyana cewa Falasdinawa ma na da hakki wajen mayar da Gabasshih birnin Jaruselem a matsayin Babban birnin kasarsu kamar yadda kasashen duniya da suka amince a matsayin hanyar kawo karshen rikicin yankin Gabas ta Tsakiya.

You may also like