An Kashe Ƴan Ƙunar Baƙin Wake Mata Su Uku A Maiduguri


chibok-girls

An daƙile kai harin ƙunar baƙin wake da wasu mata su uku zasu kai kan wani wurin da sojoji suke da akewa laƙabi da ‘Guantanamo’ dake kan hanyar Muna garage a Maiduguri.

Mai magana da yawun hukumar bada agajin gaggawa ta ƙasa NEMA, Abdulƙadir Ibrahim a wata sanarwa da yafitar yace jami’an tsaro sun harbe dukkanin matan ƴan ƙunar baƙin waken.

Ya kuma ƙara da cewa jami’in tsaro guda ɗaya ya samu rauni lokacin da yake ƙoƙarin dakatar da maharan.

“Jiya Laraba da daddare misalin ƙarfe 10:15,wasu ƴan ƙunar baƙin wake mata su uku, sunyi ƙoƙarin kai hari kan wani wurin da sojoji suke da akafi sani da ‘Guantanamo’a kan hanyar Muna garage,”yace

“An hangesu ne suna ƙoƙarin shiga harabar wurin da sojojin suke, kuma jami’an tsaro suka harbesu wanda hakan ya janyo fashewar abinda suke ɗauke dashi, yayinda suka rasa rayukansu da kuma jikkata jami’in tsaro ɗaya.”

Yace tuni aka kai gawarwakin nasu zuwa ɗakin ajiye gawarwaki dake asibitin ƙwararru na birnin Maiduguri.

 


Like it? Share with your friends!

0

You may also like