An kashe mutane 14 a hare-hare a birnin Chicago na Amurka


 

 

Mutane 14 ne suka mutu inda wasu 39 suka jikkata sakamakon hare-haren da aka kai a karshen mako a garin Chicago na Amurka.

Garin Chicago ne ya fi kowanne yawan masu aikata laifuka a Amurka, kuma a yayin bikin Halloween da aka gudanar a kasarshen makon da ya gabata an mayar da gurin kamar filin yaki. An kai hare-hare da bindiga a wajen da kungiyoyin wasanni da dama suka taru.

Yawan shan kayan maye a wajen wasannin ne ke janyo rikici a tsakanin mahalarta. A tsakanin ranakun 2-4 ga watan Yuli ma an kashe mutane 4 tare da jikkata wasu 62.

A shekarar 2016 kawai an aikata manyan laifuka 600 a Chicago.

You may also like