An kashe mutane 30 a harin bam a Afganistan


 

 

Mutane 30 da suka hada da yara kanana ne suka rasa rayukansu sakamakon harin bam na ta’addanci da aka kai a kasar Afganistan.

An kai harin ne a Firuz babban birnin jihar Gor inda ake zargin kungiyar ta’adda ta daesh ce ta kai harin.

Shugaban jihar ta gundumar Gor Nasir Khazeh ya ce, a harin da suka kai a ranar Talatar nan an kashe wani kwamandan Daesh a matsayin ramuwar gayya.

Kungiyar ta’adda ta Daesh ba ta fitar da wata sanarwa game da harin ba.58106c0a43d88

You may also like