Mutane 13 da suka hada da dalibai 7 ne suka mutu inda wasu 44 suka samu raunuka sakamakon harin da aka kai a jami’ar Amurka da ke Kabul babban birnin kasar Afganistan.
Maharan sun fara tayar da wata mota dauke da bama-bamai a kusa da jami’ar sannan kuma suka shiga cikin jami’ar tare da bude wuta kan jama’a.
Kusan dalibai 750 harin ya rutsa inda wasu suka dinga dira ta wunduna wanda hakan ya sa suka samu raunuka tare da mutuwa.
Jami’an tsaron Afganistan sun kai hare-hare mtkushe mahara wanda suka samu taimakon dakarun Amurka.
Har yanzu babu wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Turkiyya ta soki harin da aka kai a jami’ar.
Ma’aikatar harkokin Waje ta Turkiyya ta sanar da cewa, Turkiyya na tare da Afganistan a yakin da ta ke da ta’addanci.