An kashe mutane sama da 80 a Benue


photo_benue_5_alhaji_salimu_daudu_0

Gwamnatin Jihar Benue da ke Najeriya ta ce wasu da ake zargin makiyaya ne sun kashe mutane sama da 80 a kauyukan Jihar. Mai Magana da yawun gwamnatin Jihar Tahav Agerzua ya ce makiyayayn sun kai hari a kananan hukumomi 10 a cikin makwanni biyu.

Kakakin ‘Yan sandan Jihar Moses Yamu ya ce al’amura sun fara dawowa dai dai, kuma mutanen kauyukan sun fara komawa gida.

Sakataren kungiyar makiyaya ta Miyetti Allah, Baba Usman Ngarzarma ya ce zargi ne ake wa Makiyayan saboda akwai wadanda aka kashe da dama a cikinsu.

Rahotanni sun ce an kai hare haren ne a kauyukan manoman Loko da Ukum a jihar ta Benue.

Benue dai na cikin jihohin da ke fama da rikicin Makiyaya da manoma inda ko a watan Fabrairu an ruwaito mutuwar mutane kimanin 1,000 a yankin Agatu.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like