Mutane 11 aka kashe inda aka jikkata wasu 26 sakamakon hari da aka kai a ranar 2 ga Sallah a garin Ta’iz na kasar Yaman.
A wani hari da mayakan Houthi sukakai wani gida a gundumar As-Salu sun kashe mutane 5 da suka hada da yara kanana 2 da mata 3 tare da jikkata wasu 9.
A yankin Al-Zanuc kuma mayaka magoya bayan gwamnatin Yaman sun kai hari inda suka kashe mutum 1 tare da jikkata wasu 3.
A arangamar da ta balle ankashe ‘yan tawayen Houthi 5 inda wasu 14 suka sami raunuka.
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya kan bayar da taimako Jamie McGoldrick ya fitar da wata rubutacciyar sanarwa ya sake kira da a yi aiki da tsagaita wutar da aka amince da ita a watan Afrliu.
McGoldrick ya bukaci wakilin Majalisar a kasar Yaman Ismail Walid Al-Shaikh da ya taimakaya goyawa batun baya don kare afkuwar rikici a nan gaba.