An kashe Sojojin Nijar 22 yayin wani hari a jihar Tahoua


 

 

Rahotanni daga jihar Tahoua da ke arewacin Jamhuriyar Nijar, sun tabbatar da wani hari da ‘yan bindiga suka kai a wani sansanin ‘yan gudun hijira na kasar Mali, kuma sojoji da dama sun mutu a harin.

Niger Soldaten in Bosso (Getty Images/AFP/I. Sanogo)

An dai kai wannan sabon harin ne a ranar Alhamis din da ta gabata, a wani sansanin ‘yan gudun hijira na kasar Mali da ke garin Tazali a gundumar Tasara da ke jihar Tahoua. Firaministan kasar Malam Biriji Rafini ya tabbatar da mutuwar sojoji 22 amma ya ce adadin ka iya zarce haka, koda yake a cewarsa babu tabbacin fararen hula da suka mutu ko suka jikkata.

Ba a dai kai ga tantance wadanda suka kaddamar da wannan hari ba. Tashe-tashen hankula da kasar ta Mali ta sha fama da su ne dai, suka tilastwa ‘yan kasarta shiga wannan sansani. Yanzu haka dai gwamnan jihar Tahoua, Abdurahaman Mussa ya umarci sojojin Nijar da sauran jami’an tsaro da su bazama domin farautar maharan. Jamhuriyar Nijar dai ta fara fuskantar hare-hare tun bayan barkewar rikici a kasar Mali da ke makwabtaka da ita.

You may also like