An kashe wani baban ma’aikacin Banki a Yenagoa jihar Bayelsa


Banker

Wasu da ake tunanin Yan ta’adda ne sun kashe wani Ma’ikacin bankin dan  garin yenagoa a Jihar Bayelsa .yan ta’addan sun kashe Adewale Adesanya,a wani yankin  Ahoada a jihar Rivers,Adewale Adesanya ya mutune a yana da shekaru 39,ya mutu ya bar matarsa da ciki  da yara biyu da yan’uwa da dama.

Yan ta’adan su kashe Adewale Adesanya akan hanyar sa na zuwa Port Harcourt shi da abokansa biyu a motarsa,

yan ta’dan su sha kansu ne dedai wani gidan man NNPC duk da marigayin yayi kokarin tsarewa  ta hanyar shige wa daji amma sai da suka bisu har ciki suka yi ta harbin motar sai da suka sami nasarar kashe shi ,abokan iki sun sha ne ta hayar barin cikin motar tare da tserewa cikin dajin.

 

You may also like