A takaice an kashe yan fashi guda hudu a cikin sati uku a jihar Legas,kuma an kama yan fashi talatin da bakwai(37),masu sace mutane tara(9) da kuma kungiyoyin asiri (cultists) 39. comissionan yan sandan jihar Fatai Owoseni,ya bayana hakan ne yayin da yake magana da ma’jiyar labarai a hedkwatan tsaro tare da cewa an sami makamai kala-kala da motoci talatin a hanu yan fashin.
Owoseni ya kara da cewa an kama kungiyoyin asiri (cultists) lokacin da suke kokarin gudanar da kudurin su na wani bikin takwas ga watan takwas. yace alamarin ya faru ne lokacin da daya daga cikin kungiyoyin ya je bine gawan daya daga cikinsu amma a maimakon haka suka farr wa police station in Denton amma DPO da yaranshi suka samu nasaran kama mutum tara a wajen daga baya suka je suka kama mutane ashirin da daya(21).