Kashe ‘Yan Shi’a: Ba Ma Tare Da Kungiyar Izala, Shirin Su Bala Lau ne – Sheik Dahiru BauchiSheikh Dahiru Usman Bauchi yace kiran da Bala lau ya ke yi na ‘Yan Darika sun hadu da Izala Domin kashe ‘Yan Shi’a a Nijeriya maganar banza Bala lau ya ke yi dama shi azzalumi ne mai sayar da ‘yan mata a Saudiya. 

Mu bamu taba hada kai da kowa domin mu kashe wani ba ‘yan Shi’a ba sa gaba da mu kuma ba sa yakar mu ba sa zaginmu. ‘Yan Izala su ne su ke kafirta mu su ke tsine mana ko suma mu baza mu taba yakar suba balle ‘yan Shi’a da ba suyi mana komai ba.
 ‘Yan Izala sunce za su kashe yan Shi’a sai kuma Kirista sai ‘yan darika wannan shine shirin su.” Shi dai Sheikh Bala Lau yayi kira ne ga kungiyar darikar Tijjaniyya da Qadiriyya da su zo a hada karfi da karfe domin tabbatar da tsaro a kasa baki daya. 

***Majiya daga shafin Labari Daga Bauchi.

You may also like