Kashim Shettima: Kungiyoyin Agaji Suna Watanda Da Kudaden Tallafi


 

 

 

Gwamnan jahar Bornon Kashim Shettima ya zargi kungiyoyin bayar da agaji da yin watanda da kudaden da suke karba domin gudanar da ayyukan agaji.

Kamfanin dillancin Associated Press ya bayar da rahoton cewa, gwamnan jahar Borno da ke arewa maso gabashin Najeriya, ya yi kakkausar suka kan abin da ya kira almubazzarancin da kungiyoyin bayar da agaji ke yi da kudaden da suke karba domin agaza wa ‘yan gudun hijira a cikin jahar ta Borno da kuma makwabtanta.

Ya ce kungiyoyin bayar da agaji 8 ne kawai suke gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, daga cikin kungiyoyi 126 da suka rijistar gudanar da ayyukan agaza wa ‘yan gudun hijira, alhali kuwa  acewarsa, suna karbar dukkanin tallafin da ya kamata a ba su domin gudanar da wannan aiki.

Daga cikin kungiyoyin bayar da agajin da Kashim Shettima ya zarga kuwa har da asusun tallafawa kananan yara da mata na UNICEF.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like