Kaso 75 Cikin Dari na Wadanda Aka Kama Masu Satar Mutane A Kaduna Fulani Ne – El-Rufa’i


nasir-el-rufai

 

 

Gwamnan jahar Kaduna Nasir El-Rufa’i ya bayyana cewa a cikin mutane fiye da dari hudu da aka kama masu satar mutane a jahar, fiye da dari uku fulani ne masu shekaru tasakanin 18 da 30.

Ya bayyana haka ne a wata hira da ya yi da kafar yada Labarai na Muryar Amurka inda ya bayyana cewa akwai shirye shiryen da gwamnatinsa ke yi domin ta kawo karshen matsalar a jahar Kaduna, sai dai ba za a iya yin hakan ba a dawwame idan gwamnatin tarayya ba ta shigo ciki ba.

Dalilinsa shi ne, idan aka yi nasara magance matsalar a jaha guda, toh masu satar za su koma wata jahar, haka za su yi ta yi har sai an gaji an bar su.

Game da kasancewar Fulani ne yawancin masu satar mutanen, gwamnan ya ce ya kan zauna da shuwagabannin Fulani na jahar kuma ya kan fada masu cewa su tashi tsaye, domin kuwa satar mutane, da fashi da makami da satar shanu ba hali ne na fulani ba.

You may also like