Kaso 80 na malaman jihar Nassarawa basu cancanci shiga aji ba – Al-Makura


Kaso 80 cikin ɗari na malaman da suke koyarwa a jihar Nassarawa basu cancanta ba kuma idan akayi musu jarrabawar gwajin ƙwarewa to kuwa babu shakka zai fadi wanwar, Gwamna Umaru Tanko Almakura shine ya bayyana haka ranar Litinin a Akwanga.

Gwamna a jawabin bikin bude taron  da zai duba mafi ƙarancin ingancin takardar  karatun NCE, ya ce gwamnati tayi wani bincike inda ta gano cewa yawancin malaman da suke makarantun firamare da kuma na wasu makarantun Sakandire.

Al-Makura wanda ya samu wakilcin Aliyu Tijjani Ahmad, kwamishinan ilimi ya ce duk da haka gwamnatin baza tayi musu jarrabawar gwajin ba.

Ya yi kira ga hukumar dake kula da kwalejojin ilimi ta ƙasa  da kuma sauran masu ruwa da tsaki kan su yawaita sa ido domin kare bangaren daga durukushewa.

Gwamnan ya shawarci ma halarta taron   kan su mai da hankali akan  ilimin fasaha da kuma na dogaro da aki

You may also like