Kasuwar Canjin Kudade Ta Kusa Rugujewa Da Kanta –  Kemi AdeosunMinistar Kudi, Kemi Adeosun ta tabbatar da cewa nan bada jimawa ba, kasuwar musayar kudade  za ta ruguje da kashin kanta sakamakon matakan da gwamnatin tarayya ke dauka na tsaftace tsarin hada hadar kudaden waje.
Ta ce kasuwar musayar kudaden ba su da tsari kuma ba su taimakawa wajen bunkasa tattalin arzikin kasa illa kawai suna taimakawa ne kara tashin farashin kudaden waje. Ta kara da cewa, rugujewar kasuwanni za ta ba Bankuna damar gudanar da harkokinsu bisa kan tsari.

You may also like