
Asalin hoton, Getty Images
Manchester United da Paris St-Germain ka iya samun akalla fam miliyan 90 idan suka amince da saida dan wasan Napoli kuma na gaban Najeriya Victor Osimhen, mai shekara 24, a kakar wasa. (ESPN)
Arsenal ta amince da sabon kwantiragi kan mai tsaron gida na Faransa Bukayo Saka, dan shekara 21, da William Saliba, 21,di dai lokacin da Manchester City ta nuna sha’awar dan wasan Ingila. (Talksport)
Bayan fadi tashin da Chelsea ta kan sayan ‘yan wasa, yanzu hankalin ta ya karkarata kan karawa dan wasan tsakiya na Ingila Mason Mount mai shekara 24 kwantragi har zuwa shekarar 2024. Tun da fari kwantiragin dan wasan zai kare ne a cikin shekarar nan. (90min)
Makusantan mai kai hari na Gabon Pierre-Emerick Aubameyang, sun ce dan wasan mai shekara 33 ya kadu matuka da takaici kan matakin kin sanya shi wasan Champions League da Chelsea ta yi, ya kuma amince kungiyar na rara-gefe ko kai tsaye kokarin sallamarsa. (Telegraph – subscription required)
Manchester United ta amince da kara wa’adin dan wasan Argentina Alejandro Garnacho, mai shekara 18, kan kwantiragin shekara hudu. (AS in Spanish)
An samu rabuwar kawuna tsakanin ma’aikatan kungiyar Old Traffor, kan ko a bari dan wasan gaba na Ingila mai shekara 21 Mason Greenwood ya dawo kungiyar domin ci gaba da buga mata tamaula.(Guardian)
Greenwood din dai na kokarin gwada sa’ar komawa China domin farfado da kwallonsa, idan Amirka ta yanke shawarar korarsa, da zarar sun kammala nazarin da suke yi kan dan wasan. (Sun)
West Ham United da Everton za su jira har zuwa karhsen kakar wasa kafin su fara batun dauko dan wasan baya Suriname winger Sheraldo Becker, bayan kungiyar Union Berlin na tababa kan dan wasan mai shekara 27, kan barinta a watan Junairun, saboda dogon burin da suka sanyawa ran su kan wasan Champions League. (Caught Offside)
Kokarin dan wasan gefe na LA Galaxy Julian Araujo, na komawa Barcelona ya gamu da cikas, bayan hukumar Fifa ta zartar da hukuncin kammala musayar karshe kan dan wasan mai shekara 21, ko da yake an kai takardun a kurarren lokaci. (ESPN)
Manchester United na sanya ido kan tsohon dan wasan tsakiya na Amirka ajin natasa ‘yan shekara 19, Taylor Booth, mai shekara 21, jaridar Mail ta rawaito manajan kungiyar Erik ten Hag ne ke kwakwar dan wasan. (Mail)