Kayan agaji da likitoci sun isa Port-Sudan | Labarai | DWJirgin da ya taso daga birnin Amman ya sauka ne a birnin Port-Sudan da ke gabar ruwa a nisan kilomita 850 da Khartun inda a can ne fadan da ake gwabzawa ya fi tsananta. Kayayin da jirgin ya kawo sun hadar da magunguna da za su ba da damar kula da sama da mutane 1.500 daga cikin 4.599 da aka kididdige sun jikkata tun fara rikicin.  

Wannan kayan agaji dai na isowa ne a daidai lokacin da harkokin ke rincabewa a Sudan inda kungiyar likitoci na gari na kowa ta sanar da dakatar da duk wasu ayyukan jin kai sabili da barin wutar da ake wanda ya kawo katsewar aiki a kusan kashi 80%  na gidajen asibitoci da ke kasar.

Source link


Like it? Share with your friends!

0

You may also like