Kenya: Al-Shabab ta kai hari kan ‘yansanda


‘Yan sandan kasar Kenya sun yi artabu da mayakan al-Shabab sama da 50 a kan iyaka da Somaliya, to sai dai an raunata wasu jami’an ‘yan sanda.

 

 

Mayakan Al-shabab sun kaddamar da hari a wani sansanin ‘yan sanda da ke Arewa maso Gabshin kasar Kenya, ‘yan sanda da jami’an soji a Nairobi babban birnin kasar na cewa maharan sama da 50 dauke manyan makamai ne suka kai harin a kan ayarin ‘yans anda da suka kafa sansani a akan iayakar Kenya da Somaliya.

Kungiyar ta Al-Shabab dai ta yi ikirarin hallaka ‘yan sanda uku tare da kwace makamai da ma garkuwa da jami’ai biyu. To sai dai ‘yan sandan kasar Kenya sun musanta wannan ikirari, inda suka ce jami’in dan sanda guda daya ne ya samu rauni a yayin da suka yi musanyar wuta da ‘yan bindigan. Mayakan Al-Shabab dai na gwagwarmayar ganin bayan gwamnati a Somaliya. To amma kungiyar ta kaddamar da munanan hare hare da ya yi sanadiyar rayukan mutane da dama ciki har da harin da ya hallaka mutane 148 a wata jami’a a shekara ta 2015.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like