Kimanin Malamai 700 ne Za su Rasa Ayyukansu a Jahar Jigawa


www-aarewa24news-com_muhammad-abubakar-badaru

 

Gwamnatin jahar jigawa ta kaddamar da sabon kwamitin tantancewa na musamman da aka dorawa alhakin zakulo malaman bogi, malaman da ba sa zuwa aiki, da wadanda suka tafi karin karatu, suka kuma gama amma basu dawon kan aiki ba.

A bisa wannan tantancewa, ana tsammanin cewa akalla malamai 700 ne ke fuskantar barazanar rasa ayyukansu a kananan hukumomi 27 da ke fadin jahar.

 

Tantancewa za ta bayarda kaima musamman ga bangaren malaman da suka tafi karin karatu, suka ki dawowa. Akwai rahotannin cewa al’amarin malaman da ke karo karatun ya sanya gwamnatin jahar soke komawa yin karatu yayin da ma’aikaci ke kan aiki.

Shugaban ma’aikata na jahar, Mohammaed Inuwa Tahir ya bayyanawa manema labarai cewa akwai ma’aikatan da ke shafe kimanin shekaru 14 zuwa 15 suna karatu, ba sa zuwa aiki kuma suna karbar albashi, inda ya kara da cewa gwamnatinsu ba za ta lamunci irin wannan kasala da rashin adalci ba.

You may also like