Wani me gidan haya da aka bayyana da suna, Idemudia Obamonyi,ya kona gidan mahaifinsa da ya mutu ya bar masa bayan da mutanen dake haya a gidan suka gaza biyan kuɗin haya.
A cewar rahotanni shaguna sama 20 ne a gidan, dake layin Owobo bayan kasuwar Oba dake Benin babban birnin jihar Edo.
Mutane dake wurin ne suka jiyo Idemudia yana fadin cewa a bari gidan ya kone tunda shi baya amfana da gidan.
Wani mazaunin yankin mai suna,Ifaluyi Obasogie ya ce wannan abu ne da ba a saba jin irinsa ba ace mai gidan haya ya kona gidansa da kansa “Mun ga mutane suna riƙe shi yana cewa a bari gidan ya kone, bana samun ko kwabo daga shi.”
Wani dake haya a daya daga cikin shaguna dake a gidan,Justice Aigbekhan, ya ce sun biya kuɗin hayarsu amma Idemudia ya cigaba da tambayarsu kudi wai yana son yin bikin binne mahaifin nasa.
Tuni dai jami’an tsaro suka damke shi.