KIRISTOCIN DAKE ZAUNE A MAHAIFAR ANNABI ISA SUN SOKE KIRSIMETI DON ADAWA DA AMURKA KAN JERUSALEM 



Kiristocin mahaifar Annabi Isa (AS) na garin Nazareth sun soke bukukuwan kiristimeti don nuna bacin ransu ga matakin da Amurka ta dauka na amincewa da birnin Jaresalem a matsayin Babban birnin kasar Isra’ila.

Mai Unguwan birnin na Nazareth, Ali Salam ya ce matakin Shugaban Amurkan kan Jaresalem ya dusashe farin cikin bukukuwan Kiristimeti na wannan shekarar inda ya ce a wannan karo za a kunna fitilu ne a itatuwa kawai. Birnin Nazareth dai na daga cikin wuraren da mabiyan addinin Kirista ke ziyarta a yayin aikin ibadarsu.

You may also like