Gwamnan jihar Binuwai, Samuel Ortom da ‘yan majalisarsa sun nemi gwamnatin tarayya kan ta gaggauta cafke Shugabanin kungiyar Miyaetti Allah Kautal Hore bisa zarginsu da hannu wajen kisan gillar da aka yiwa wasu ‘yan kabilar Tibi a jihar.
Gwamnan da ‘yan majalisar sun gabatar da wannan bukatar ce a lokacin da Ministan Harkokin cikin Gida, Abdurahman Dambazau ya kai ziyarar jaje ga wadanda suka rasa ‘yan uwansu a lokacin harin. A cewar Gwamnan, tun bayan da jihar ta kaddamar da dokar hana kiwo, shugabannin kungiyar suka yi barazanar daukar matakin gurgunta shirin dokar.