Kisan kan da yafaru a birnin Onitsha bashi da alaka da jam’iyar APC – yan sandaRundunar yan sandan jihar Anambra ta wanke jam’iyar APC daga zargin da ake mata na hannu a rikicin da yafaru ranar Juma’a a garin Onitsha da ya jawo mutuwar mutane biyu.

Kafofin sadarwar zamani sun cika da rahoton labarin da ke cewa mutane 3 aka kashe a Onitsha ranar Juma’a wacce tayi daidai da ranar da jam’iyar APC ta kaddamar da yakin neman zaben dan takararta a zaben gwamnan jihar, Tony Nwoye,  da za a gudanar cikin watan Nuwamba.

A wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar yan jihar, Nkeiruka Nwode, ta fitar kuma aka raba wa manema labarai, rundunar ta karyata jita-jitar, inda tace babu kam shin gaskiya a labarin.

Ta ce mummunan abin da yafaru bashi da alaka da taron APC, wanda ya samu halartar mai girma mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo, gwamnonin jam’iyar APC 12, ministoci 17 da kuma yan majalisar ƙasa 25 da sauran mashahuran mutane.

Wasu makiya jam’iyar ne suke so su yi amfani da rikicin wajen cimma wani buri na siyasa ta hanyar alakanta jam’iyar da rikicin.

Ya yin da  ta bayyana abin da yafaru sakamakon hatsaniya tsakanin wani direban mota da yan sanda wanda ya jawo mutuwar direban.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like