Shugabar hukumar kare hakkokin bil adama na kasar Sudan ta Kudu Yasmin Sooka ta ce abinda yake afkuwa a wannan kasar ya yi kama da kisan karen dangin kasar Ruwanda.
Yasmin ta yi wannan jawabin ne bayan ta share kwanaki 10 tana zagaya kasar, inda ta ce ko shakka babu a kauyuka da dama na kasar Sudan ta Kudu,ana ci gaba da kisan kare dangi a boye.kana ta kara da cewa ko shakka babu saura kiris bala’in da ya afku a Ruwanda ya sake faruwa a wannan kasar.
Kisan kare dangin kasar Ruwanda wanda ya barke a shekarar 1994,ya zama sanadiyar mutuwar akalla mutane 800.000.
Shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva kiir ya karyata wannan batun a yayin wani taro da ya halarta a birnin Johannesburg na kasar Afirka ta Kudu,inda ya ce maganar da majalisar dinki duniya ta yi game da kasarsa, ba komai ba ce face zuku ta malle.