Wani ɗan sanda mai muƙamin Kofural a ranar Talata ya kashe abokin aikinsa mai muƙamin Sajan a wata mashayar giya dake garin Gulak a ƙaramar hukumar Madagali ta jihar Adamawa.
Lamarin ya faru ne bayan da sajan ɗin ya sayi giya a hannun wata mace da ake tunanin budurwar kofural ce.
Mazauna yankin sun ce Koporal Bala Adamu ya saki kunamar bindigar sa bayan sun kaure da cacar baki inda ya kashe Sajan Timothy Emmanuel nan take.
Shedu sun ce Timothy wanda ke aiki da rundunar ƴan sandan kwantar da tarzoma ta 13 dake Makurdi amma aka turo shi aiki na musamman a Madagali inda ya sayi burkutu ta ₦100 daga wurin matar wacce ta kasance budurwar Kofural Adamu.
Matar wacce ta shawarci Kofural kan ya biya ta kuɗinta a hannu tunda tana binsa bashin wasu kuɗaɗe amma ya dage sai ta ƙara masa bashin ₦100 a kai.
Sun ƙara da cewa lokacin da Adamu ya hangi budurwarsa tana magana da Timothy sai kishi ya kama shi inda ya garzayo ya zuwa wurin cikin fushi inda ya gargadi sajan ɗin da ya ƙyale masa budurwa.
Bayan yar gajeriyar cacar baki Adamu ya daga bindigarsa ya saki harbi kafin a kama shi tare da budurwar tasa.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sanda a jihar Adamawa, Othman Abubakar ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kama mai kisan ya yin da aka ajiye gawar a dakin ajiye gawarwaki ya yin da aka fara bincike.