Ko Ali Nuhu Ne Ya Aikata Irin Laifin Da Rahama Sadau ta Yi Sai Mun Koreshi –  MOPPAN


A wata tattaunawa da aka yi da sakataren kungiyar MOPPAN Salisu Mohammed (Officer) ya ce, “har yanzu Rahma Sadau korarriya ce daga finafinan Hausa, ba kuma za ta dawo ba”.

Sannan kuma ya kara da cewa “ko Ali Nuhu ne ya aikata irin laifin da jarumar ta yi a yanzu, za mu kore shi. Kuma ba mu tattauna da shi kan cewa za a dawo da Rahma cikin harkar fim ba.
A kwanakin baya dai a wata hira da kafafun yada labarai suka yi da Ali Nuhu game da korar Rahma da aka yi daga masana’antar fim, ya nuna cewa wannan hukuncin da a ka yi mata ya yi tsauri, sannan kuma ya nuna cewa za a tattauna da Kungiyar MOPPAN domin ta sassauta wannan hukunci. 
Babban Sakataren kungiyar Salisu Muhammad, ya tabbatar da cewa, an koreta sannan ya kara da cewa, ba za a dawo da ita hakar wasan kwaikwayon ba.
Sakataren ya  kuma bayyana cewa, shima Ali Nuhu a cikin wasu finafinansa na baya yayi makamancin abin da ta yi na rungume-rungumen mata ko kuma sunbatarsu. 
Ya ci gaba da cewa, ba a dauki mataki akan Ali Nuhu bane sakamakon wannan kungiya ba ta da wasu tsare tsare da kuma hukunce-hukunce da suka yi hani da haka a waccan lokaci, amma idan ya ce zai yi abinda yayi a baya, to lallai za a koreshi kamar yadda a ka kori Rahama Sadau. 
“Ali Nuhu ya yi irin wadannan laifuka a shekaru biyu zuwa uku da suka wuce, a lokacin ba a sabunta dokokin kungiya ba ne, ba kuma mu yi taron masu ruwa da tsaki ba ne, domin daga taron ne muka fitar da sabbin tsare-tsare da dokokin shirin fim.” 
“A wannan taro Rahama ta na wurin, Ali Nihu kuma ya samu labarin abin da aka yi a taron. Amma tabbas ka sani idan Ali Nuhu ya sake irin abin da yayi a baya za mu kore shi kamar yadda muka kori Rahama Sadau a finafinan Hausa”.


Like it? Share with your friends!

0

You may also like