
Asalin hoton, Getty Images
Yaƙi da cin hanci da rashawa na cikin muhimman abubuwan da Shugaban Najeriya mai barin-gado Muhammadu Buhari ya ce ya fi bai wa fifiko a tsawon shekara takwas na mulkinsa.
An yi ittifakin cewa matsalar ta cin hanci ita ce babban abin da ya yi wa ƙasar mafi yawan jama’a a Afrika tarnaƙi wajen samun cigaba ta kowace fuska.
Babu shakka idan akwai wata siffa da ta jawowa Shugaban Najeriyar farin jini a wajen talakawan ƙasar, ita ce gaskiyar da suka yi imanin yana da ita, kuma tunanin cewa shi ne kaɗai zai iya cire wa ƙasar dabaibayin da cin hanci da rashawa ya yi mata na tsawon gwamman shekaru.
Haka kuma yaki da matsalar ta cin hanci, na daga cikin manyan alkawuran yakin neman zaɓensa a duk tsawon shekaru 12 da ya kwashe yana neman shugabancin ƙasar.
Ayyana Muhammadu Buhari a matsayin wanda ya ci zaɓen shugaban ƙasa na shekara ta 2015, ya zo kamar burin ƴan ƙasar ne ya cika na samun wani mai ceto ƙasar daga cikin halin taɓarɓarewar al’amuran attalin arziki da take ciki wanda aka danganta da rashin gaskiya wajen ta’ammali da dukiyar ƙasa.
“An samu gagarumin cigaba”
Babban mataimaki na musamman kan harkokin watsa labarai ga Shugaba Buhari Malam Garba Shehu, ya ce gwamnatinsu ta samu gagarumin c gaba a yaƙi da cin hanci da rashawa a tsawon shekaru takwas da suka shafe kan mulki.
Ya ce mulkin Shugaba Buhari ya kawo canji yadda ƴan ƙasar ke kallon cin hanci da rashawa.
Inda ya ce kafin hawansa mulki ko magana ba a yi kan cin hanci da ake tafkawa a ƙasar.
Asalin hoton, GARBA SHEHU
Malam Garba Shehu ya ce a karkashin mulkin Buhari ne aka kawo tsarin zuba kuɗi a asusu na bai ɗaya na Gwamnatin Tarayya, wato TSA.
Inda ya ce hakan ya taimaka wajen magance matsalar cin hanci saboda duk wani kuɗi da ya shiga asusun gwamnati ana iya ganinsa.
“An rufe dukkkan asusu wanda aka buɗe ba bisa ka’iba ba, an ƙarfafa hukumomin da ke yaƙi da cin hanci, an kuma ba su ƴancin cin gashin kansu. EFCC da ICPC na aiki ba tare da tsangwama ba, an kuma karfafa ofishin mai binciken kuɗi na ƙasa,” in ji Garba Shehu.
Ya kuma ce an kafa hukuma mai bayar da shawara kan yaki da rashawa da kuma fitattun lauyoyi da ke kawo wa gwamnati rahotanni kan batun rashawa har ma ana kaiwa gaban majalisar tarayya.
Kakakin ya ƙara da cewa gwamnati ta yi gwanjon manyan kadarori da aka gina su da kuɗaɗen haram, inda ya ce a tsawon shekarar da ta gabata, ICPC ta ƙwato kuɗin da ya kai naira miliyan dubu 67 a hannun ma’aikata da suke zarewa.
Mai taimaka wa Shugaba Buharin ya ce ita ma EFCC ta samu nasarar ƙwato dala miliyan 386 a shekarar da ta gabata.
Dangane da batun kin cewa ko uffan da Shugaba Buhari ke yi kan muƙarrabansa da ake zargi da aikata cin hanci, Garba Shehu ya ce hakan ba gaskiya ba ne.
“Ba a taɓa samun wata gwamnati da ta ɗauki shugaban kotu na ƙasa ta je ta gurfanar da shi ba, an cire minsitan kuɗi da kuma hukunta ma’aikata da dama waɗanda aka samu da laifi a satar duƙiyar ƙasa,” in ji shi.
Yaya hukumomin yaƙi da cin hanci ke kallon batun?
Hukumomi da ke yaki da cin hanci a Najeriya, sun ce tun bayan ɗarewar Shugaba Buhari kan mulki, sai ƙara samun nasara ake yi a yakin da ake yi da matsalar.
A jawabin da ya yi wa manema labarai a watan Disamban bara, kan inda aka kwana a aikin da hukumarsa ke yi, shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC Abdurasheed Bawa, ya ce sun samu nasarar da ba a taɓa samu ba wajen kame da kuma hukunta waɗanda ke satar dukiyar kasa.
Bawa ya ce a shekara ta 2016, wadda ta kasance shekarar Buhari ta farko a kan mulki, EFCC ta samu nasara kan shari’o’i 195.
Ya ce a shekarar da ta gabata lokacin da ya karɓi ragamar hukumar, sun samu nasara kan mutum 2,220 da suka gurfanar a gaban kotu.
Abin kuma da ya ce nasara ne a yaki da cin hanci da rashawa.
“An samu koma-baya”
Sai dai masu fafutukar yaki da cin hanci da rashawa a ƙasar na ganin cewa ko an samu nasara a yakin ta wasu wuraren, ba ta kai yadda jama’ar ƙasar har da na kasashen waje suka yi tsammani ba.
Wakilin kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta duniya ta Transparency International a Najeriya, Kwamared Auwal Musa Rafsanjani, ya ce duk da cewa an ɗan samu nasara a wani ɓangare, amma fa lamarin ƙaruwa ya yi.
“Akwai wuraren da ake cin hanci a yanzu babu tsoron Allah, ƙaruwa aka samu na cin hanci ba raguwa ba. Ana satar maƙudan kuɗaɗe da kadarori karkashin wannan gwamnati,” in ji Rafsanjani.
Ya ce babu ta inda za a yaki rashawa a wajen da jami’an gwamnati da muƙarrabai ba su ma da sha’awar batun duk da cewa ita ce aƙidar shugaba Buhari.
Ya ce ya dace a samu haɗin-kan ministoci da gwamnoni da jami’an ƙananan hukumomi da kuma darektoci kafin a samu nasarar yaki da cin hanci.
Asalin hoton, Auwal Musa Rafsanjani
Rafsanjani ya ce cin hanci ya mamaye ɓangarorin gwamnati da dama musamman wajen sayen kuri’u da sayen muƙamai da kuma bayar da kuɗi kafin a ɗauki mutum aiki.
Ya ce bai kamata a ce gwamnati ta sasanta da jami’ai da suka saci kuɗi ba saboda zaluntar jama’a suka yi.
Ya ce matsalar cin hanci da rashawa ta janyo rashin ababen more rayuwa da taɓarɓarewar harkar ilimi da lalacewar asibitoci da rashin tsaro da kuma rashin ruwan sha a cikin al’ummomi.
Bugu da kari kuma, ga alamu iƙirarin mahukunta a Najeriyar na samun nasarar yaki da cin hanci da rashawa a wannan marrar fiye da kowane lokaci a baya, ya yi hannun riga da alkalumman da hukumar ta Transparency International ke fitarwa duka shekara kan matsayin kowace kasa a yakin da cin hanci.
Idan aka yi la’akari da alkalumman hukumar daga shekarar ta 2015 lokacin da Shugaba Buhari ya hau gadon mulki zuwa bara, Najeriya ta samu cibaya a yaki da cin hanci daga ta 136 a duniya a shekarar 2015 zuwa ta 154 a shekara ta 2021.
Sai dai wani abu da ake gani a salon yakin da cin hanci da gwamnatin Buhari da ba a saba gani ba, shi ne barin hukumomin yaki da almundahana su kama tare da gurfanar da manyan kusoshin gwamnati ba tare da yin katsalandan ba.