
Asalin hoton, Getty Images
Liverpool ta karbi bakuncin Arsenal a wasan mako na 30 a Premier League da za su kara a Anfield ranar Lahadi.
Gunners ta yi nasarar cin 3-2 a wasan farko a gasar da suka fafata ranar 9 ga watan Oktoban 2022.
Arsenal tana matakin farko a teburin Premier League da maki 72, yayin da Manchester City wadda ta ci Southampton ranar Asabar mai maki 67 tana ta biyu.
Liverpool, wadda aka fitar da ita a Champions League da FA Cup tana ta takwas a teburin babbar gasar tamaula ta Ingila da maki 43.
Rabon da Gunners ta ci Liverpool a lik tun karawar da Mikel Arteta ya buga wasan da Arsenal ta ci 2-0 a Anfield a 2012.
A karkashin Jurgen Klopp, Liverpool ta yi nasara a karawa shida baya da suka fuskanci juna a Anfield, inda Liverpool ta ci kwallo 22, gunners ta zura hudu a raga.
Sai dai wannan karon Liverpool ba ta kokari, wadda take da tazarar maki 29 tsakaninta da Arsenal, mai fatan lashe Premier League a bana na farko run bayan kakar 2003/04.