Ko Dan Kabilar Igbo Ya Zama Shugaban Kasa 2019 Ko Kuma Mu Kafa Kasar Biafra A 2020 – Ohanaeze Ndigbo  Bangaren matasan kungiyar al’ummar Igbo ta Ohanaeze Ndigbo, sunyi kira da kodai a bawa dan kabilar Igbo shugaban kasa a shekarar 2019 ko kuma su tabbatar da yantacciyar kasar Biafra a shekarar 2020.

  Kungiyar ta bayyana wannan matsaya ne cikin wata sanarwa da suka fitar bayan taron da suka gudanar a garin Enugu. 

 Sanarwar ta samu sa hannun babban sakataren kungiyar Okwu Nnabuike.

Amma kungiyar tace dan arewa zai iya samun mataimakin gurbin mataimakim shugaban kasa. 

Kungiyar matasan sun ce sun cimma wannan matsaya ne ganin yadda yan arewa suke adawa da kiran da ake na a bawa yankunan kasarnan kwarya-kwaryar cin gashin kai, da kuma umarnin da wasu kungiyar matasan arewa suka bawa al’ummar kabilar Igbo na su fice daga yankin kafin ranar 1 ga watan Oktoba. 

Matasan na kungiyar Ohanaeze sunce shugaban kasar Najeriya  da yafito daga kabilar Igbo ne kawai zai iya shawo kan yan kungiyar IPOB ta Nmandi Kanu da kuma MASSOB ta Uwazuireke. 

A karshe kungiyar tayi kira ga al’ummar kabilar Igbo dake zaune a kasashen waje dasu bada gudunmawarsu domin tabbatar da nasarar wannan matsaya da matasan suka cimma. 

Kiran na matasan na zuwa ne bayan da mukaddashin shugaban kasa yafara ganawa da masu fada aji daga yanknan biyu a kokarin da ake na shawo kan lamarin. 

You may also like