
Asalin hoton, Getty Images
Shugaban TikTok Shou Zi Chew zai fuskanci tambayoyi na ƙwaƙwa daga ƴan majalisar Amurka
Yayin da ake ci gaba da ka-ce-na-ce da kuma zargi a kan manhajar TikTok, abin da zai iya kai wa ga Amurka ta haramta amfani da shafin na China, yanzu hankali ya karkata ga matashin shugaban wannan shafi da ya mamayi duniya, Shou Zi Chew.
A ranar Alhamis 23 ga watan Maris din nan ne matashin mai shekara 40, ɗan ƙasar Singapore ya bayyana a gaban ƴan kwamitin kula da harkokin makamashi da kasuwanci na majalisar wakilan Amurka, a game da tsaro da kare sirrin masu amfani da shafin da kuma zargin da ake yi wa manhajar kan alaƙa da gwamnatin China.
Babu wani abu da aka sani sosai game da yadda shugaban yake gudanar da aikinsa ko kuma girman ainahin ikon da yake da shi a kamfanin.
Wadda aka fi sani da shafin ita ce babbar jami’arsa Vanessa Pappas, wadda kuma a watan Satumba na 2022 ta ƴan majalisar dokokin Amurka suka titsiye ta da tambayoyi a kan yadda bayanan Amurka ke kwarara zuwa China ta manhajar.
Wani rubutu da aka yi a jaridar New York Times a watan Satumbar na bara ya yi nuni da kalaman da tsofaffin shugabannin kamfanin na TikTok da Bytedance suka yi cewa Mista Chew ba shi da wani iko sosai wajen tafiyar da kamfanin manhajar ta TikTok, wanda ya nuna cewa Zhang Yiming wanda ya ƙirƙiro ByteDance shi ne ke tafiyar da kamfanin.
To amma kuma yanzu TikTok na sanya Mista Chew gaba-gaba a harkar kamfanin yayin da yake fuskantar zargin alaƙa da gwamnatin China.
A wata wasiƙa da kamfanin ya aika wa ƴan majalisar dokokin na Amurka a watan Yuni na bara, kamfanin ya jaddada cewa yana gudanar da aikinsa ne ba tare da wata alaƙa ko katsa-landan daga babban kamfanin da ya mallake shi ba wato ByteDance.
A takardar, kamfanin ya dage wajen jaddada wa ƴan majalisar cewa shugaban ba ɗan China ba ne ɗan Sigapore ne kuma a can yake da zama.
An haifi shugaban ya kuma tashi a Singapore, inda ya halacci makarantar ƴaƴan masu hali da ake koyarwa da harshen China, kuma yana jin Ingilishi da yaren Mandarin na China sosai.
A lokacin aikinsa na yi wa ƙasa hidima a rundunar sojin Singapore, a matsayin hafsa.
Mista Chew ya samu digirinsa na farko a fannin tattalin arziƙi daga Jami’ar London kafin ya tafi Jami’ar Harvard, inda ya samu digirinsa na biyu.
Haka kuma ya yi aikin sanin makama a kamfanin shafin Facebook a lokacin kamfanin bai bunƙasa ba.
Wasu rahotanni sun ce, yayin ɗan taƙaitaccen aiki na shekara biyar a kamfanin zuba jari na DST, inda ya jagoranci ayarin wasu ma’aikata waɗanda suka kasance masu hannun jari na farko a ByteDance a 2013.
Haka kuma ya yi aiki a matsayin jami’in banki kan harkokin zuba jari a Goldman Sachs tsawon shekara biyu.
Bayan nan Mista Chew ya taka muhimmiyar rawa a babban kamfanin waya na China Xiaomi, inda ya kasance babban jami’in kuɗi na kamfanin kuma shugabansa na harkokin kasuwanci na duniya.
Bugu da ƙari shi ne ya jagoranci sanya kamfanin wayar a kasuwar hannun jari a 2018.
Daga nan ya tsallaka zuwa kamfanin ByteDance a watan Maris na 2021, inda ya zama mutum na farko da ya riƙe matsayin babban jami’in kuɗi a katafaren kamfanin ya.
Bayan wata biyu kacal, sai ya zama babban shugaban kamfanin mahnajar TikTok, bayan da mai wannan muƙami Kevin Mayer, ya yi murabus ba zato ba tsammani sakamakon neman tilasta sayar da kadarorin kamfanin da ke Amurka da gwamnatin Trump ke neman yi.
Babban Ƙalubale
Yanzu dai Mista Chew na fuskantar ƙalubale mafi girma a rayuwarsa ta aiki da TikTok, inda ƴan majalisar dokokin Amurka ke son kamfanin ya sayar da hannun jarin reshensa na Amurka ko kuma a haramta shi a ƙasar.
Wannan batu ya zama abin ja da kiki-kaka ga ita ma gwamnatin China.
Kafar yada labarai da gwamnati ta Global Times a wani nazari da ta yi bayan ƙuri’ar jin ra’ayin jama’a ranar Talata, ta nuna cewa matakin neman haramta shafin na TikTok, abu ne da yanayin mugunyar siyasar Amurka ya haifar, kuma zai kasance ya saɓa tsarin kasuwanci mai walwala.
Rahoton ya ƙara da cewa kasancewar shafin TikTok daga Amurka yake, hakan a wajen jami’ai da ƴan siyasar Amurka wani laifi ne babba.
Yadda yake fuskantar bincike da matsi ta ɓangarorin biyu, a ƴan watannin nan shi ma Mista Chew ya yunƙuro.
A watan Fabarairu da ya wuce shi ma ya yi shafinsa na TikTok @shou.time , inda yake nuna wasu abubuwansa na rayuwa, kusan shekara ɗaya ke nan da hawa kujerar shugabancin kamfanin manhajar.
Mabiya shafin na Mista Chew su kusan 18,000, sun ga yadda yake halartar wasannin kwallon zari-ruga na Amurka Super Bowl da na ƙwallon kwando na NBA.
Da yadda yake haɗuwa da fitattun mutane kamar Bill Murray, har ma wani lokaci yana neman yin rawa da mawaƙiya Ciara.
Ya kuma ratsa kafofin yaɗa labarai inda a wasu hirarraki da ya yi yake nuna cewa shi mai sha’awar wasan ƙwallon lambu ne wato Golf kuma mai sha’awar Kevin Hart ne mai barkwanci.
Shugaban mai ƴaƴa biyu, wanda yake auren Vivian Kao shugabar wani kamfanin zuba jari ya ce ba ya barin ƴaƴansa su yi amfani da TikTok saboda ƙanana ne.
A kwanakin nan ya riƙa tattaunawa da manyan kafofin yaɗa labarai na Amurka, inda yake jaddada cewa TikTok ba shi da wata barazana ga muradin Amurka.
Har ma kuma yana roƙo ga masu amfani da shafin waɗanda ke Amurka da su taimaka.
A wani hoton bidiyo da ya sanya a shafin kamfanin na TikTok ranar Talata da yamma a Washington ya nemi su gaya masa abin da suke so ya faɗa wa ƴan majalisar dokokin na Amurka.
A bidiyon wanda mutane sama da rabin miliyan suka so, ya ce, wannan lokaci ne mai muhimmanci garemu.
”Wannan zai iya raba dukkaninku mutane miliyan 150 da TikTok.”